Mansur Usman Sufi?
The author Mansur Usman Sufi was born in Kano in 1992 in Rijiyar Lemo area, he attended boarding school in Sheik Adam katibi in Rijiyar Lemo area.
Student Daiba. Mansur Usman Sufi studied under Islamic scholars where he memorized the great Qur'an with the knowledge of hadith.
Currently, he is not married but he intends to start writing in 2010 where he started writing a book called MUGUN NUFI.
In 2013, he published his first book called Tafarkin Tsira.
The book was very well received in the school even though at this time there is another star of the famous writer
Abdul'aziz Sani Madakin Gini from this he published the book Kogon Annoba which is also very popular in the school and even the famous journalist of the Shasha BBC Hausa, a former employee of North Radio,
Read it after he published the book JARUMAN DUNIYA, which is more popular than others, and Hajiya Nabila Muktar Uba also read it at North Radio in Kano State, Northern Nigeria.
In 2014, he became the financial secretary of the Tsintsiya Writers Association, and attended many writers' meetings in the northern states of Nigeria.
In 2016, he released the book
KANGING BAUTA which was typed by Shatan Writers Company and published by Sufi Publishing Company as a complete book.
After that, Mansur Usman Sufi became the secretary of the Arewa author forum of Nigeria. in 2022 we will have a place in the group of Hausa writers of Kano state.
BASARAKE
Sabon Littafin Yaki
Rubuta Labari
Mansur Usman Sufi
Littafan yaki.com.ng
08137237071
BABI NA FARKO
Ƙasaitacciyar kasuwar ta cika ta batse da manya da ƙananan 'yan fatake, maza da mata haɗe da ayarin baki da birane da manyan ƙasashen duniya.
Duk inda mutum ya kai duban shi zai ga jama'a na ta kai komo suna hada-hadar siye da siyarwa cikin kwanciyar hankali da lumana.
Fiye da shekaru ɗari bakwai wannan kasuwa takasance cibiyar cinikayya a yankin ƙasashen Larabawa baƙaƙen fata, shekarun da suka shuɗe kasuwar tana ci ne duk bayan wata shida, ma'ana a shekara sau biyu take ci, amma kasancewar FATAKE na yin tafiya mai nisan zango, daga sassan duniya hakan ya sanya aka canja tsarin ya zamto cewa a duk lokacin da wani ayari suka iso birnin Zawatul-dinar za su iya gudanar da cinikayyar su. Sai dai duk shekara ana cin kasuwar ƙarshen zango.
Bakomai ne ya sanya birnin Zawatul-dinar ya samu wannan shahara ba sai bisa dalilai guda huɗu.
Na farko shi ne sun bunƙasa a arzikin noma da kiwo, yawan al'umma masu kyawun ɗabi'u, tarin ZARATAN JARUMAI masu Juriya a FILIN DAGA, abu na ƙarshe shi ne samun adalin sarki mai jiɓintar damuwar al'ummarshi.
Sarkin da ke riƙe da sarautar birnin ana yi masa laƙabi da Hubrul-Zaman. Sarki Hubru kasance kyakkyawar saurayi ma'abocin kwarjini, KARFIN DAMTSE kuma mashahurin attajiri.
A wannan lokaci gaba ɗaya ƙasashe da biranen dake nahiyar sun shaida cewa babu MASHAHURIN SARKI kuma GWARZON MAYAKI tamkar shi.
Duk waɗannan abubuwa da sarki Hubru ya mallaka dukiya, ƙarfin rundunar mayaƙa sun zamo tamkar kumfar kogi, domin kuwa ba shi magani da zai zamto halifan shi a bayan shi.
Bai taɓa soyayya ba kuma bai yarda da ita ba, yana ganin cewa babu komai a cikin soyayya face shirme da shashanci.
'Ya'yan manyan sarakuna, bokaye haɗe da attajirai sun bayyana sirrin zukatansu na buƙatar mallakar Hubru a matsayin abokin tarayya, amma sai ya sanar da su cewa ba zai taɓa yin soyayya ba har ƙarshen rayuwar shi.
Bisa al'adar sarki Hubru duk lokacin da yake cikin nishaɗi ya kan yi ɓadda-kama ya shiga izuwa dajin dake birninshi domin ya yi farauta.
Wata rana daga cikin ranakun da Huburul-zaman ke fita farauta, tafe yake a bisa ingarman doki, yana sanye cikin baƙaƙen tufafi ya rufe fuskarshi da rawani idanuwanshi kaɗai ake gani.
A gadon bayanshi yana rataye da wani rantsattsan KWARI DA BAKA a kwiɓin cinyarshi yana makale da wata sharɓeɓiyar takobi a cikin kubenta.
Ya wanzu yana ratsa wani daji mai cike da duhuwar bishiyu, duwatsu, ƙoramu da sarƙaƙiya.
Lokacin da ya iso gindin wata bishiya sai ya ja linzamin shi ya tsaya cak! Ya sakko ƙasa ya ɗaure shi a jikin bishiyar sannan ya kunna kai izuwa cikin daji yana mai zare bakanshi.
Sannu-sannu sarki Huburul-zaman ya shafe tsawon rabin sa'a yana tafiya ba tare da ya ji motsin koda ɓera ba ballantana ya ji kukan tsuntsu, al'amarin da ya yi matuƙar ba shi mamaki kenan kuma ya ɗaure mashi kai kenan domin tsawon shekaru goma yana fitowa wannan farauta hakan bai taɓa faruwa ba ya ce a ranshi, shin ko dai halittun dajin sun farga da shigowar shi shi yasa suka nemi maɓuya. Wani ɓangaren a zuciyarshi kuma ya ce da shi anya kuwa ba maƙiyin ka ba ne ya yi maka tarko domin ka faɗa.
Amsar tambayoyin da Huburul-Zaman ya kasa bawa kanshi kenan, kawai ya ci gaba da kutsa kai cikin dajin har yazamana ya shafe sa'a ɗaya cif! A dai-dai wannan lokaci ne ƙishi da yunwa suka fara addabar shi, amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta GWARZON ƘARNI sai ya ƙara himma.
Yana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai ya hango wata kyakkyawar barewa ta sunkuyar da kanta tana shan ruwa a ƙorama.
Nan take farin ciki ya cika zuciyarshi ya zare kibiya guda ɗaya a cikin kwanson dake rataye a gadon bayanshi ya saka a cikin bakanshi ya ja ya taɓe da dukkan ƙarfin shi sannan ya harba. Kibiyar ta tafi cikin matsanancin gudu tana mai keta iska ya durfafi barewar, lokacin da ya zamana tazarar dake tsakanin kibiyar da ita bai huce kamu haɗu ba, kwatsam! Sai wata kibiyar daban ta bayyana ta kaɗe ta Huburul-Zaman.
Al'amarin da ya fargar da barewar kenan ta ranta a na kare.
Al'amarin da ya fusata Huburul-Zaman kenan ya fusata ainun cikin takaici ya rufa ma barewar baya suka tasa tsere.
Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce inda babu ƙasa nan ake gardamar kokowa.
Ana fara wannan artabu ne wani abun mamaki ya fara wakana, yazamana cewa duk irin ƙarfin gudu na sarki Hubru amma ya kasa cimma barewar.
Lokacin da aka shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu ana wannan tsere nan take Ƙarfin gudun sarki ya fara raguwa saboda yunwa da ƙishi da suka ƙara tsananta gare shi.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai ya ji hucin hucewar wata kibiya ta saman kanshi. Kafin ya farke ta soke wannan barewa a gadon bayanta ta wuntsila ƙasa matacciya ko shurawa ba ta yi ba.
Al'amarin da ya sanya Huburul-Zaman ya ja ya tsaya ya yi turus cike da matuƙar al'ajabi, yana mai duba gabas, yamma kudu da arewa ko zai ga makashin barewar ya bayyana amma shiru kake ji.
Kawai sai ya durfafi inda gawar barewar take domin ya sarrafa naman ta ya yi kalaci ko ya yi maganin yunwar da ta addabe shi
Kwatsam! Sai ya ji busassun ganyayyaki na motsawa, alamun da nuni da cewa akwai wani abu mai rai da yake shirin bayyana gare shi.
Daga can sai wani jarumi ya yi fitar burgu daga cikin duhun bishiyun dajin daf da inda barewar take tamkar an harbo shi daga cikin baka.
Littattafan yaki da Mansur Usman Sufi ya wallafa
TAFARKIN TSIRA
JARUMAN DUNIYA
KOGON ANNOBA
KANGIN BAUTA
KARSHEN ZALUNCI
SARAUTAR MUTUWA
FATAUCIN BAYI
TAKOBIN DAUKAKA
SARKIN SADAUKAI
GOGA SHA FAMA
KARNI UKU
KARYA DA GASKIYA
WRITER Contact | Top Novels Author |
---|---|
1 | Kogon Annoba |
2 | Jaruman Duniya |
3 | Goga Sha Fama |
4 | Kangin Bauta |
5 | ƙarshen Zalunci |
6 | Fataucin bayi |
7 | Sarautar Mutuwa |
8 | Sarkin Sadaukai |
9 | Annoba Dar |
Post a Comment