Kangin Bauta book 1 by Mansur Usman Sufi


Book Contact INFORMATION FOR THIS BOOK IN THE YEAR 
Book KANGIN BAUTA BOOK 1
Author MANSUR USMAN SUFI
Uploader Mrs Sarkin Marubutan Yaki
Image Credit SUFI GRAPHICS
Size 124
File TXT
Date 20 April 2023
Group
Tages Adventure


Book information 

Download Kangin Bauta book 1 complete hausa adventure story written by me, Mansur Usman Sufi in text format. Recently I shared book 1 and 2 for free. So now, is book 3. Download and read it shared by your author, Sarkin Marubuta Sufi.

BOOK DESCRIPTION

Kyawawan samari ne majiya karfin damtse su uku, mai matukar kwarjini da ban tsoro. Na farkonsu yana rataye da waɗansu zaratan takubba guda biyu a gadon bayanshi kuma ya kasance mai matuƙar kaurin jiki fiye da 'yan uwanshi.

Saurayi na biyu yana dauke da wani irin KWARI DA BAKA mai daukar hankali,jikinsa a murde yake ya tara kwanji,

kallo daya zakayi masa kafahimci cewa ya fi sauran yan uwansa kirar sadaukantaka.

Na ukun kuwa yana ɗauke da dauke da dogon nashi mai baki biyu,

bakin yakasance daga farkon sa yayi fadi daga karshe yayi tsini ya fitar da baki biyu.

Babu abin da zai burge ka ga samarin sama da yadda suka yi shigar yaƙi iri daya saka

kuma suna zaune abisa jajayen dawakai ingarmu.

Samarin uku suna tafiya ne acikin wani daji ma,abincin dogayen bishiyoyi,koramu,

tare da kwazazzabai.gaba daya yanayin dajin ya banbanta da sauran dazuzzukan da idanuwa suka saba gani.

Domin hatta kwari da tsuntsayen dake cikin sa abin tsoro ne.awasu lokutan sai kaga tsuntsaye na dauke da fuskokin bil,adama,hatta bishiyoyin dajin suna canza launi zuwa launi,

Tabbas dajin yana da matukar kwarjini ga duk jarumin daya tsinci kansa acikin sa dolane ya razana

Haka dai zaratan samarin uku suka cigaba da tafiya adajin Babu alamun razani atattare da fuskokinsu Lokacin da suka shafe tsawon sa,a daya da dakika talatin suna tafiya acikin dajin,a dai dai wannan lokaci ne suka fara hango wani katafaren gida kwaya daya jal adajin,

Al,amarin da yayi matukar basu mamaki kenan suka ce acikin zukatan su.taya za,ace wannan kasurgumin daji ace an gina wannan kerarrran gida a cikinsa.

Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan, suka cigaba da tafiya,

Da isar su bakin gidan suka tarar da gidan ya kasance tankameme Tamkar gari guda.gaba daya ginin anyi shine da waɗansu manyan duwatsun wuta wadanda ido bai taba gani ba,

Katangun gidan sun kasance masu tsawon gaske.akwai ƙatuwar kofa guda daya jal mai tsawo da kauri inda za,a sanya karti majiya karfi mutum hamsin bazasu iya ture ta.

Nanfa samarin suka yi cirko-cirko suna nazarin kofar tsawon dakika arba,in dayansu bai ce uffan ba.

Daga can sai daya daga cikin su wanda ake kira da suna Hilwas yayi gyaran murya yace "yaku 'yan uwana yanzu mene ne abinyi?

Gashi yanzu mun iso gidan boka kimraz,naji ajiki na cewa dukkan baiwar da muke da ita bazata yi mana wani amfani ba face muyi Amfani da fasahar da muke da ita."

Koda jin wannan batu sai sharwas yayi caraf ya tari numfashin Hilwasa

yace"Ni shawarar dazan bamu muyi tunanin hanyar da zamu bude Wannan kofa,

kunsan masu iya magana na cewa abari ya huce shi ke kawo rabon wani, kuma da zafi-zafi a kan daki karfe."

Duk wannan tattaunawa da akeyi kahzib yayi shiru bai ce kala ba. Fuskar sa cike da damuwa,

Kahzib yayi gyaran murya yace"yaku abokaina nifa ba wannan abu ne damuwata ba.

shin kun mantane cewa rayuwar iyayenmu tana hannun sarki shardasu.

A cikin ku wane yake da tabbacin sarki shardasu zai cika alkawarin daya daukar mana idan muka mallako masa abubuwan da yake buƙata na bamu fansar rayukan iyayemu.

me yasa baza muyi tunani me yasa baza muyi tunani akan nemo musu maganin dazai warkar da lalurar dake samun su ba?

Sa,adda kahzib ya zo daidai nan azancen sa sai jikin Hilwasa da sharwas yayi sanyi.

Kuma hankalinsu ya dugunzuma ainun suka zurfafa izuwa kogin tunani,

Su dai wadannan samari sun fito ne daga Wani birni da akewa lakabi da BAITUL-NA'IM.

dalilin daya baro dasu daga gida shine kamar haka:-

***

Birnin baitul-na,im yakasance kasaitaccen birni daya shahara a fannin noma, kasuwanci.

wanda ya haɗar da attajirai da manoma.kuma suna da ZARATAN MAYAKA masu juriya a filin daga. Sarkin da yake rike da Sarautar wannan birnin ana kiransa da shardasu ibn furais,

Sarki shardasu yakasance Gwarzon mayaki mai tarwatsa maza afilin fama.

mutum ne mai son abin duniya dadin dadawa kuma yakasance AZZALUMI nagaban kwatance.

Domin duk shekara a birnin sa ana noma abinda bokaye da masu hasashe suka tabbatar da cewa zai iya ciyar da kasashen dake nahiyar na tsawon shekaru biyu amma saboda zaluncin sa sai dai ya siyar da abincin ga manyan kasashen da ke wata nahiyar daban Duk yawan abin da mutum ya noma zai kasashi gida Biyar ya dauki daya kaso hudun na sarki shardasu ne.

hatta dabbobi bai kyale ba duk shekara a kwai kason sa aciki, Sai da ya Zamo duk faɗin nahiyar babu attajiri kamarsa.

Mahaifan Waɗannan samari uku sun kasance bayi ne ga sarki shardasu asali sarki shardasu ne ya cinye kasar su da yaki ya ribato su a matsayin fursunonin yaki.

A tarihin samartakar su ba,a samu jarumai kamar su ba a can ƙasar su Mahaifan su sun samu lalurar dake jikin sune saboda bautar da suke yi a karkashin sarki shardasu.

Mahaifin Hilwasa ana kiransa da suna Rukaisu , Rukaisu ya samu lalurar makantane saboda aikin ƙera dukkan nau,ikan kayan yaki,kofuna,da sauransu abubuwan da ake sana'anta su da zinariya da jauhari. Tunda Rukaisu yake Wannan aiki nasa ba,a taba samu ya ƙera wani abu ba yadda sarki ya buƙata ba amma

saboda wata rana an samu akasi ya kera wadansu kofuna ba yadda aka umarta ba ya sanya aka soke masa idanu da wasu kibiyoyi na wuta idanunsa suka makance kuma aka aikashi izuwa kurkuku.

Mahaifin sharwas kuwa ana kiransa da suna Rauzil ya kamu da ciwon kuturtane a hannayen sa da ƙafafuwan sa saboda aikin dafa sarki shardasu ruwan wanka wata rana rauzil ya kammala dafawa sarki ruwan zafi a bahon wanka bayan ya kammala zuba turaruka da sabulai masu kanshi,

sai ya umarci wadansu kuyangi da sukai ruwan izuwa kewaye.

Jim kadan sai ga sarki shardasu ya fito daga kewayen fuskarsa a murtuke tamkar an aiko masa da sakon mutuwa.

kawai sai ya damki gashin kan Rauzil yana janshi akasa har izuwa inda wani ƙaton kasko yake a turakar sa.

Kaskon yana dauke da wani tafashasshan ruwan zafi mai kauri baƙi baƙi.

kawai sai sarki shardasu ya kama hannayen Rauzil ya tsomasu acikin kaskon.

Tun Rauzil yana kwarara ihu har takai bana iyawa sai dai hawaye kawai yake zuba a idanunsa.lokacin daya fito da ƙafafuwan take naman jikinsu ya zagwanye Babu tausayi afuskar sarki shardasu ya damki hannayen Rauzil ya motsa akaskon,

Hakika komai rashin imanin mutum idan yaga yadda Rauzil yake kwarara ihu yana zubar da hawaye dolane ya tausaya masa sai da naman jikin hannayen ya zagwanye sannan ya yi jifa dashi gefe guda

Rauzil na fitar da numfashi sama-sama tamkar zai sheka barzahu daga nan aka kaishi izuwa kurkuku yazamo gurgu baya iya tafiya sai dai rarrafe

Mahaifin kahzib kuwa ana kiransa da suna Hashim Shi kuma ya samu lalurar kurumta ne

saboda wani laifi da ya yi wa Sarki shardasu ya dunga dura masa garwashin wuta a baki yana hadiyewa

Matayen su hasham kuwa sai suka kasance cikin matukar bakin ciki tare da kewaye mazajen su dare da rana Bayan shudewar wannan al,amari ne da kwanaki arba'in sai sarki shardasu na zaune a fadar sa.

ALSO RELATED POST

KARNI UKU BOOK 1

SARAUTAR MUTUWA BOOK 1

FATAUCIN BAYI BOOK 1

Download

Post a Comment

Previous Post Next Post