Yar mulki latest Hausa novels by


Book Contact INFORMATION
Book YAR MULKI
Author Hafsa
Uploader mrs littafan yaki
Image Credit Sufi Graphic
Size 12.kb
File TXT
Date 7 APRIL 202
Group zauren Majalisar marubuta
Tages romanti

PROLOGUE
     Cikin nutswa drivers din suke tukin,gudun kar ran Amal ya baci,motoci ne guda biyar ajere,gabadayansu bakakene,motar tsakiya itace wadda Amal ke ciki,akwai biyu agaba biyu a baya wadanda duk body guards din Amal ne aciki.

     Haka suka cigaba da tafiya,tana faman basu umarnin yadda take son tukin yakasance cikin tsiwa,da kuma mulki,suna xuwa kofar gidan,mai gadin yayi xumbur ya mike ya bude gate din tacewa drivern kai tsaya cikin tsiwa,ta xuge glass ta kalli mai gadin a wulakance,tace,banace maka idan na dawo kadaina batamin lokaci wajen bude gate ba?? Ya tsugunna yace kiyi hakuri ranki ya dade,baxan sake ba,Amal tace idan ka bari na kara maka magana a karo na biyu a ranar xakabar gidannan.ta bada umarni drivern yaja motar xuwa harabar gidan.

       Motar da Amal ke ciki na tsayawa,bayin ta guda biyu suka fito,kowacce a gefen ta guda daya,suna ta faman gyara mata riga wadda ke jan kasa,suka shiga cikin gida.

       Bangaren momy ta nufa,tana shiga momy tace my Amal kindawo?,Amal ta karasa ta kwanta a cinyar momy tace ehh,momy ta shafa kanta,tace Amal meya faru ne? Naga duk ranki a bace,yau kuma waya taba min ke? idon Amal ya ciko da kwalla tace momy nifa vanason mai gadin nan wlh,duk sai ya batawa mutane lokaci kafin ya bude gate,momy tace akan wannan kawai kike nema kiyi kuka? So kike ki tayarmin hankali,kawai dan kuka baya miki wahala? Kinga kiyi shiru xansa mai martaba,ya canja masa aiki acikin gidannan.momy ta kalli jakadiya dake gefenta tace kawowa Amal ice cream,jakadiya tace to rankiya dade,ta fita cikin hanxari,,sannan momy ta mai da idanun ta kan Amal tace,nasa akawo miki abinda kike so,ki daina bata ranki kinji.
Amal tayi shiru alamar ta gamsu da rarrashin da momy tayi mata.

Post a Comment

Previous Post Next Post