Book Contact | INFORMATION FOR THIS BOOK IN YEAR 2024 |
---|---|
BOOK | GWARAZAN JIYA |
AUTHOR | MANSUR USMAN SUFI |
UPLOADER | MRS LITTAFIN YAKI |
IMAGE CREDIT | SUFI GRAPHICS |
SIZE | 23KB |
FILE | TXT |
Date | 30 APR 2024 |
Group | ZAUREN LITTAFIN YAKI |
TAGES | ADVENTURE |
Description Book
Jarumar tana sanye cikin fararen tufafi masu yalwa tun daga ƙasa har sama, hatta dokin da take kai ya kasance ingarma fari sol! Gwanin ban sha’awa, tafiya take a cikin wani ƙasaitaccen daji ma’abocin dogayen bishiyu, duwatsu, da tsaunika, sai da ta shafe tsawon zango uku tana tafiya babu sassauci.
Lokacin da ya zamana cewa zango haɗu ya shuɗe sai dokinta ya fara sasssarfa, alamun cewa ya fara gajiya da tafiya. Kawai sai ta ja linzamin dokin ta tsaya tsak! Ta kama ta sauko ƙasa ta ɗaure dokin a wata bishiya.
Kawai sai ya ɗauko salkarta domin ta yi amfani da ita, nan take taga babu babu ruwan a cikinta, nan fa hankalinta ya dugunzuma ainun domin tana buƙatar ta yi alwala domin gudanar da ibada.
Tana cikin wannan hali kwatsam! Sai ta hango wata ƙorama a nesa kaɗan da inda take, cikin matuƙar farin ciki ta durfafi inda take, sa’adda ta isa ta tsugunna ƙasa domin ta ɗeɓi ruwan, kwatsam! Bazato babu tsammani sai taga waɗansu irin girɗa-girɗan dakaru masu ƙirar samudawan farko suna tasowa daga ƙasan ƙoramar, waɗansu na fitowa daga maɓuyar su, suka yiwa jarumar ƙawanya, adadin dakarun ya kai guda dubu uku da ɗoriya, dukkanin su suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, fusakunsu a murtuke suke tamkar basu taɓa dariya, kaico! Haƙiƙa waɗannan dakaru sun kasance ababan tsoro ga duk wata halitta mai numfashi, domin suna ɗauke da miyagun makamai dangin Gatari, Takobin, Kwari da baka, Sungumi, kai har da ma abin da idanu ba su taɓa gani ba.
Koda jarumar tayi arba da dakarun sai ta miƙe tsaye zumbur ta zare takobin dake gadon bayanta aka fara kallon-kallo tsakanin su.
Nan fa mayaƙan suka cika da matuƙar mamaki kuma suka fusata ainun, ba komai ne ya basu mamaki ba sai bisa ganin yadda jarumar ta iya yin GABA DA GABA da su babu alamun tsoro ko firgici a tattare da ita. Abin da ya fusata su shine tun da suka fitowa wannan sana’a ta fashi da makami ba su taɓa yin gamo da jarumi mai dakakkiyar zuciya tamkar wannan jaruma ba.
In da ace mutum yana tsaye a wannan waje zai ga yadda jarumar ta fuskanci mayaƙan, dole ne ya jinjina mata ya tabbatar da cewa ta cika MACE MAI KAMAR MAZA.
Ana cikin wannan hali ne sai kawai wani narkeken ƙato mai ƙarfi na Allah ya isa ya fito daga cikin mayaƙan, yana da faffaɗan ƙirji mai cike da curi-curin tsoka, idanuwanshi jajur suke tamkar garwashi wuta, girmanshi ya kai na haɗe dakaru biyu waje guda, a ƙugunshi yana yana ɗauke da wata ɗamara da aka sana’anta ta da zallar a zurfa.
Garjejen ƙaton ya tako lafta-laftan ƙafafuwanshi ya matso daf da inda jarumar take tana huci tamkar kububuwa, ya buɗe tafkeken bakinshi mai kama da bakin rijiya ya dakawa jarumar tsawa, cikin wata irin kakkausar murya mai kama da haushin kare ya ce “ya ke wannan rafkananniya a cikin jerin JARUMAN DUNIYA ki yi sani cewa kin faɗa TARKON AZABA, domin kin tafka babban kuskure da kika shiga gonar shugaban ‘yan fashin wannan nahiyar, sadauki AUSUR IBN DAISHAM, yanzu ba tare da ɓata lokaci ba zan aike da ruhinki izuwa barzahu na mallake dukkanin abin da ke tare da ke, don haka sai ki shirya ga maza nan bisa kan k.
Koda gama faɗin hakan sai shugaban ‘yan fashi Ausur ya yiwa yaranshi inkiya ta wutsiyar idanu take suka yi ɗauki kan jarumar suna ihu da kururuwa mai firgitarwa, koda ya rage saura taku biyar su cimma ta sai kawai ta dako wawan tsalle daga inda take tsaye tamkar an harbo ta daga baka ta sauka a tsakiyar mayaƙan, ana haɗuwa aka rugumtsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini ban tsoro gami da tashin hankali.
Wohoho! Haƙiƙa mai ƙarfi sai Allah ya isa, nan fa ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, ƙarar karafniyar ƙarafa, haɗe da ihu da kururuwar MAZAJEN DUNIYA ya cika dodon kunne.
Nan fa jarumar ta zamto tamkar shaiɗaniya a tsakanin mayaƙan, ta wanzu tana shayar da su azabar KAIFIN TAKOBI gami uƙubar yaƙi, kuma tana yaƙin ne cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance.
Wani barde daga cikin mayaƙan ya yi ihu da kururuwa mai firgitarwa ya kaiwa jarumar sara da gatarinshi, cikin baƙin zafin nama ta sunkuiya ya sari iska, sannan ta taso sama ta sanya hannun da baya ɗauke da makami ta kama wuyan barden ta murɗe da dukkanin ƙarfin ta, take wuyan shi ya yi ƙara ya karye ji kake ruƙus! Ƙas ta jefar da gawarshi ƙasa ko shurawa bai yi ba.
Kafin shuɗewar sa'a ɗaya jarumar ta kashe fiye da dakaru ɗari biyu ta jikkata ɗari uku, koda ganin irin mummunar ɓarnar da ta yi masu sai sauran mayaƙan suka yi ɗauki kanta, suna ihu da kururuwa mai firgitarwa DANDAZON MAYAƘA, ana haɗuwa waje ya sake rincaɓewa da baƙin gumurzu.
Sassan jikkunan bil’adama suka dinga shawagi a sararin samaniya suna zuba ƙasa tamkar ruwan su ake yi daga saman, hankakan mutuwa ya wanzu yana kai komo wajen ɗaukar rayuka.
Duk wannan artabu da ake yi sadauki AUSUR yana tsare a gefe guda yana kallon abin da ke wakana, ya yin da yaga yadda tawagarshi ke yin muguwar hallaka sai takaici da baƙin ciki suka turnuƙe zuciyarshi, jikinshi ya kama tsuma yana ƙyarma, kawai sai ya dakawa yaranshi tsawa da sake afkawa jarumar.
Lokacin da sa'a ɗaya da daƙiƙa hamsin ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi, sai ya zamana cewa jarumar ta kashe fiye da rabin ‘yan fashin, ya zamana cewa duk inda mutum ya kai duban shi babu abin da zai gani face dakarun kwance fulu-fulu cikin jini babu kyan gani.
Sa’adda shugaba Ausur ya ga cewa idan aka ci gaba da wannan gumurzu wankin hula zai kai shi dare, ma'ana jarumar za ta ƙarar da baki ɗaya dakarunshi. Sai kawai ya ɗauko wani ƙaho a aljihun rigarshi ya kafa a bakinshi ya busa da ƙarfi, faruwar hakan ke da wuya sai ga waɗansu sabbin mayaƙa na musamman kimanin dubu biyar suna ratsowa ta duhuwar bishiyu suna haɗe da sauran mayaƙan, aka ci gaba da rugumtsumewa da masifaffan yaƙi.
Nan fa jarumar ta zamo tamkar an ajiye ƙwayar gero a cikin dandazon tururuwai, saboda yadda mayaƙan suka yanyame ta.
Jarumar ta ci gaba da saran ‘yan fashin tana zubar da su a ƙas, tamkar tana karkaɗe busassun ganyayyakin bishiyu a lokacin hunturu, JINI DA ƘASA suka cuɗanya waje guda. MUTUWAR SADAUKAI ta yawaita.
Ana cikin wannan artabu ne wani hamshaƙin barde daga cikin mayaƙan ya jefowa jarumar gatarinshi, gatarin ya taso cikin iska cikin matsanancin gudu, koda ya rage saura kamar kamu uku tsakanin shi da jarumar, sai kawai jarumar ta waiga bayanta cikin zafin nama ta gwaninta ta cafe gatarin sannan ta wurgawa badakaren, take gatarin ya sare wuyan barada biyu suka faɗi ƙasa matattu ko shurawa ba su yi ba.
Kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA yafi SARKIN ƘARFI sai mayaƙan suka samu nasarar zubar da a ƙasa, tana fitar da numfashi sama-sama tamkar zata sheƙa barzahu.
Koda ganin wannan nasara sai shugaba Ausur ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta tamkar ba zai daina ba.
Abin tambaya anan shine daga ina wannan jaruma take, kuma ina za ta je.
Dalilin hakan shine kamar haka:-
Post a Comment