Book Contact | INFORMATION FOR THIS BOOK IN THE YEAR |
---|---|
BOOK | Yadda Kaddarata Ta So |
AUTHOR | Salma Ahmad Isa |
UPLOADER | MRS SUFI NOVELS |
IMAGE CREDIT | SUFI GRAPHICS |
SIZE | 532kB |
File | txt |
Date | 02 MAY 2024 |
Group | Zauren Sufi Novel |
TAGES | Life Story |
- He is wearing a jersey like a cricket, green color on the back of the shirt is written 'TAFEEDAH', the jersey pants are on his body which goes down to the ground and it is also green, there is a white line on the side of the pants, his leg is wearing protective gear with crickets is wearing on their feet (batting pad), his hand is wearing a cricket glove, his head is wearing a cricket helmet, his hand is holding a cricket bat (cricket stick).
- He took his position, he was waiting for Joakim to throw the ball to him, he sent the ball to him and hit the ball with all the strength that God had given him, the ball flew up, everyone raised their heads and waited to see where it would land, but it did not fly down. They don't have to cross the line, send their team members to shout at him and call his name. appear.
- Very long, and white, white, not like Africans, white like Indians, his hair is like his Indian origin, it lay on his head, in a high fade cut, and a razor part on the side, there is a thin beard A single strand of hair came down from his forehead and joined the one he knew and surrounded his mouth. Comparing his beauty to me is timeless, his kind is called the end of discussion, a kind of beauty for him, what is amazing, what attracts the attention of what to look at him, his eyes go no matter what attracts attention on his face, which is light blue color say.
- He was standing where he put his cricket kit bag, he was putting his cricket kit in it, the helmet was the last thing he had in the bag, and then he zipped the bag.
- He reached and opened the small pocket of the bag where he kept his phone and the p-cap he came with. that shows him that there is something happening in the hospital, he put the phone in the pocket of his pants, then he put the bag on his back.
- And then he took the way out of the war, his steps were slow and proud, which shows that he is of the royal blood, although he does not know that, but the kingship is in his blood, or I believe that if the people have raised his hand and he also raised his hand, he is not very eloquent, but he is also kind, and everyone knows him there.
- He said that the playground is not far from his house, that's why he used to come to the foot, whether it was in the estate, there is a tarmac, so he followed the road that would connect him to his house, wherever he went, if there were girls, they would be afraid, son Tafida is the kind of person that not every young woman will see him and turn away, God bless him with the popularity of girls, his walk is just a sight to behold.
- With that, he came to the door of his house which is the same as the other houses in their block, from the gate there is a thin board written 'DR. ESHAAN AUWAL TAFIDA, B3 NO 122'.
- His right hand raised the one he was wearing a digital watch, and from the top of the watch was a stamped bracelet, which contained the text 'TAFIDAH'.
ST NICHOLAS HOSPITAL,LAGOS NIGERIA*
“wai ina dr. ESHAAN din ?”
wani likita da ake kira da dr. ola ya tambayi nurses din dake bakin aiki, yayinda ya fito daga dakin da aka kwantar da wani mara lafiya da aka kawo musu asibitin, nurse chinaza ce tace.
“ sir Saturday, dr. baya zuwa ranar weekend”
“ai nasan da hakan, amma dolene yazo, aikine na ceton rai, dan haka ku kirashi yazo da gaggawa”
“ok dr”
joke ta faɗi tana juyawa, hanyar office dinsu ta nufa dan wayarta tana can
“ah-ah joke to where ?”
joke ta tsaya tana kallon dr. khabir babban abokin dr. eshaan
“Offce namu zanje na ɗauko wayana, zan kira TAFIDA ne”
“wani abun ne ya faru ?”
ta gyada kai “ eh an kawo wani pertinent ne kuma ana bukatarsa”
“ok jeki kawai bari na kira shi”
“ok”
ta juya zuwa inda ta fito, shi kuma khabir ya fito da wayarsa daga cikin aljihun lap coat din dake jikinsa ya nemo lambar TAFIDA a jerin contact din dake wayarsa ya aika masa da kira.
*ALARO CITY LEKKI, LAGOS, NIGERIA*
Alaro city wani haddaden estate ne wanda za'a iya kira da gari, rukunin gidajene masu kyau, tsarin ginin gidajen kamar a kasar turai, kuma a kowani block tsarin gudajensu iri daya ne, sunada masallaci da church, super market, filin wassani,bpolytechnic, asibiti, makaranta duka a ciki.
****
Sanye yake da Jersey irinta cricket, green color a bayan rigar an rubuta 'TAFEEDAH', wandon Jersey din ne a jikinsa wanda ya sauka har kasa shima kuma green ne, anyi layin fari a gefen wandon, guwar kafarsa sanye cikin abun kariya da ƴan cricket ke sakawa a kafarsu ( batting pad), hannunsa sanye da safar hannu irin ta yan cricket, kansa sanye da helmet na cricket, hannunsa rik'e da cricket bat (sandar cricket).
Ya ɗau matsayarsa, yana jiran joakim da zai cillo masa ƙwallon, aiko yana cillowa ya takarkara ya daki kwallon da duka karfin da allah ya hallita masa shi, ƙwallon ta tashi sama, kowa ya daga kai yana jiran yaga inda zata sauka, bata tashi sauka ba sai a ketaran layin da aka shata, aiko ƴan team dinsu suka saka ihu sukayi kansa suna kiran sunan sa, dama sun sani idan har wasa da TAFIDAH ne basu da haufi, yana murmushi ya cire helmet din dake kansa, ai nahin surar fuskarsa ta bayyana.
Dogone sosai, kuma fari, fari ba irin na Africans ba, fari irin na asalin Indians, ga sumar kansa irin ta asalinsa wato india, ta kwanta a kansa lif, cikin askin high fade, ga kuma razor part a gefe, ga wani bakin kwataccen gashi daya sauko tun daga sajensa ya had'e da wanda yake habarsa ya kuma zagaye bakinsa, kammanin fuskarsa sune suke tabbatar da asalinsa na ba'indiye. Kwatanta irin kyan da yake dashima b'ata lokacine, irinsa ake kira da end of discussion, wani irin kyau gareshi me ban mamaki, me kuma daukar hankalin me kallonsa, kwayar idonsa tafi komai jan hankali a fuskartasa, wadda ta kasan ce light blue color ce.
***
Tsaye yake a inda ya aje cricket kit bag dinsa, yana saka kayan cricket din nasa a ciki, helmet itace a bu na karshe da yasaka a cikin jakar, sannan yayi zipping jakar.
Hannu ya kai ya bide karamin aljihun jakar inda ya aje wayarsa da kuma p-cap ɗin daya yazo da ita, p-cap ɗin wadda aka rubuta TAFIDAH a samanta ya saka a kansa sannan ya buɗe wayar tasa, missed calls ya gani daga Khabir, hakan ke nuna masa cewa akwai wani abun dake faruwa a asibiti, wayar ya saka a aljihun wandon dake jikinsa, sannan ya sab'a jakar a bayansa.
Sannan ya kama hanyar fita daga wajen wassanin, cikin da takunsa na kasaita da izza da kuma aji, wanda yake nuna cewa shid'in jinin sarauta ne, duk da bayasan hakan, amma sarautar a jininsa take, ko ina yabi idan da mutane sai sun ɗaga masa hannu shima kuma ya ɗaga, dan ba wani sosai ya cika magana ba, amma kuma yanada kirki, kuma kowa ya sanshi a wajen.
Kasan cewar filin wassanin da gidansa babu nisa hakan yasa yake zuwa a kafa, ko ina a estate din shimfide yake da kwalta, dan haka ya bi titin da zai sada shi da gidansa, ko ina ya wuce idan da ƴan mata sai sun ƙyasa, dan Tafida irin mutanannane wanda ba kowace budurwa bace zata ganshi ta kauda kai ba, Allah ya masa farin jinin ƴan mata, tafiyarsa ma kawai abar kallo ce.
Da haka ya karaso kofar gidan nasa wanda yake sak iri daya da sauran gidajen dake block ɗinsu, daga jikin gate din kuma akwai wani siririn allo da aka rubuta ‘DR. ESHAAN AUWAL TAFIDA, B3 NO 122’.
Hannunsa na dama ya ɗago wanda yake sanye da digital watch, daga saman agogon kuma a kwai wani stamped bracelet, me dauke da rubutun 'TAFIDAH'.
Aagogon ya dan daddana nan take gate din ya zuge zuwa gefe, kai ya saka cikin kyakyawan gidan nasa, yana shiga gate ɗin ya kulle, ginin benine mai hawa daya, daga gefen ginin kuma glass ne tun daga sama har kasa, tun daga waje idan ka kalli saman gidan zakaga kujerun dake laye a saman rufin gidan, a parking lot din gidan kuma motoci uku ne, Audi RSQ 8-R, Honda elevate da kuma marsidis benz.
Ƙofar entrance din ya bude ya shiga ciki, babban falone a farkon kofar, wanda yake dauke da set din ɗima-ɗiman kujeru, wata kofar glass ce ke facing din kofar shigowar, wadda zata sada mutum da garden din gidan, wanda kuma yake a backyard din gidan, stairs din da zai kai mutum sama kuma yana cikin falon, daga kasa idan ka daga kanka zaka iya hango ƙofofin dakunan gidan, domin corridor din dake kunshe da dakunan a ba katanga bace, glass ne aka saka kuma shima gajere, ƙofofu hudune a parlon, wadda suka kunshi kitchen, dakin guga, gym, sai store amma ba na kayan abinci ba, na aje kayan amfanin gida.
Stairs ya fara takawa wanda zai kaishi zuwa dakinsa, wanda yafi kowani ɗaki cikin dakuna uku dake gidan girma, komai na cikin dakin dark an light blue ne, sai kuma fari tun daga kan bad sheet, blanket, pillows, curtains, carpet harda set din kujerun dake dakin da dai sauransu.
Cricket kit bag din bayansa ya sauke ya ajeta a inda ya saba ajewa, ya cire wayarsa daga aljihu ya dora akan gado, ya karasa inda dayar wayar tasa take chargy ya zare chargyn ganin ta cika ya ajeta itama a inda ya aje dayar.
Ya dawo gaban dressing mirror ya cire agogon dake ɗaure a haannunsa ya aje a kan table din, ya cire p-cap din dake kansa ya ratayeta a jikin hat stand din dake kusa da dressing mirror din,Sannan ya shiga wanka.
Bayan wani lokaci ya fito daure da towel, yana goge jikinsa da wani towel din, a gaban dressing mirror din ya tsaya ya jona hand dryer ya shiga busar da sumar kansa, saida ruwan dake jikin sumar ya tsane sannan ya dauko hair straightener dinsa ya shiga taje gashin nasa, sannan ya dauko man daya saba shafawa sumar tasa ya shafa nan take ta soma kyalli, ya gyaggyara zaman gashin dake takiyar kan nasa, dan a gefe da gefen kan nasa da kuma baya babu sumar sosai, an asketa sbd askin high fade din da yayi.
Jikin faffaɗar lokarsa ya koma, wadda ta kusa cinye fadin katangar da take jiki, ya bude kofa daya, saida yayi taku daya biyu kafin ya isa shiga cikin wardrobe di, dan lokar ƴar bangoce, kuma kamar closet, manyan kaya ya zabo wani plane yadi golden color, ya saka a jikinsa ya fito daga wajen hannunsa rike da hula tangaran, yana gyara karin hular.
Saida yazo gaban mirror ya saka hular a kansa sannan ya feshi jikinsa da turare, ya dawo wajen shelve din dayake aje takalmansa ya dauko wani bakin moccasin ya saka a kafarsa, sannan ya juyo ya dauki wayoyin nasa a inda ya ajesu, ya dauki keyn daya daga cikin motocinsa ya fito, benz ɗinsa ya shiga ya wuce ST NICHOLAS HOSPITAL.
A babbar rumfar da a samanta aka rubuta Dr. ESHAAN AUWAL TAFIDA yayi parking, ya fito yana ta gaisawa da ma'aikatan dayake haduwa da su, har ya kai office ɗinsa, kuma tun kafin ya shiga cikin office ɗin nasa yaci karo da khabir, hannu ya bashi sukayi musabihi suna gaisawa sannan yace
“ai na kiraka baka d'auka ba, kuma dama nasan kana filin cricket”
“ saida muka gama wasan naga kiran naka ai, shine na shirya na taho”
yayi maganar cikin yaran hausa, wadda ba zaka taba tunanin yasan hausarbama ballantana ya iyata, ga kuma suturar dake jikinsa, wadda take kara dangantashi da hausawan
“me ke faruwa ?”
ya faɗi cikin muryarsa ma abociyar kamewa da nutsuwa,me taushi da kuma zurfi
“wai wani mara lafiya ne aka kawo shi, kuma ana bukatarka, shine dr. ola yace a kiraka”
“ok to muje na ganshi”
Daga haka suka wuce inda aka kwantar da mara lafiyar, dubashi yayi yaga kuma matsalar tasa tana bukatar tiyata, dan haka ba b'ata lokaci suka shiga dakin tiyatar dashi.
Cikin nasara akayi aikin aka gama, ya fito yana bawa nurse bayanan magungunan da ya kamata a bawa mara lafiyar, office dinsa ya shiga, daga nan ya zarce banɗaki.
Hannunsa ya shiga wankewa a gaban sink, bayan ya gama kamar da akace kalli mirror idansa yakai wajen, gabansa ne yayi mummunar faɗuwa, sbd abinda ya gani, hankalinsa yakai kololuwa wajen tashi, a dugun zume yayi gaban mirrorn yana dudduba fuskar tasa, ƙwayar idansa wadda take light blue itace ta rikiɗe ta koma ja, wannan abun ba baƙo bane a wajensa, amma kuma a kwanakin nan abun ya fara yawa, a da sai yayi wata nawa abun bai tashi ba, amma yanzu kusan kullum sai ya tashi, yanzu har takaima idan nasa na sauya kala ba tareda yaji a jikinsa ba, hannu yakai ya riƙe kansa tareda lumshe idanunsa, addu'a yake san yayi amma bakinsa yayi masa nauyi kamar kullum, yasani dole abun nasa ne zai tashi, haka ya bude idonsa ya ƙarasa ya fita waje, da hannunsa yayi nuni ga inda wayoyinsa suke nan take suka tashi suna yawo a iska har suka karaso kan hannun nasa, da kyar ya samu ya fice daga asibitin, kuma yanata jugewa hada ido da kowa, dan kada wani ya samu yaga kalar idon nasa.
Cikin motarsa ya shiga, ya sakata a lock, ya dafe kansa a jikin sitiyari, yanajin abinda ya saba ji a duk lokacin da abun zai tashi, bayan wani lokaci ya dago da kan nasa, ya fita hayyacinsa gaba daya, kwayar idanun nasa ta ƙara komawa ja, bakinsa ya buɗe nan take wasu dogayen fiƙoƙi suka sauko daga haƙwaransa na sama, ya rikiɗa ya koma dodo, me ban tsoro, gaba daya jikinsa rawa yake, sai ya fara fisge-fisge, yana barazanar kifar da motar, wannan shine halin dayake tsintar kansa a ciki a wasu lokutan.
*BINYAMINU USMAN POLYTECHNIC, HA'DEJIA, JIGAWA STATE NIGERIA*
Wasu ƴan matane guda biyu tafe akan titin fita daga makarantar, yanayin tafiyar sune kadai zai nuna maka cewa a gajiye suke gaba ɗaya.
Ɗaya bakace sanye da atamafa da kuma mayafi, yayin da ɗayar ta kasance fara amma ba sosai ba, sanye take da hijabi har kasa, wanda ya 'boye atamfar dake jikinta.
Post a Comment