PROLOGUE
Allah ya tsinewa duk wache ta dibarmin ruwa." Bata rufe bakinta ba wata mata naji ta chafe zanchen ta hanyar cewa yatsinewa uwarki, shegiya mara hankali."
Kutt, cewar yarinyar da bata wuce shekara goma sha hudu ba .
"Uwa ta fa kikace, yamah sunanki? Saude koh, to wlh yau kintabo bala'i da kudinki, kar kiga wai kina matar baba na na kyakeki wlh sai kinyi dakinsani zagina da kikayi."
Ta fadi tana murguna baki.
"Eheee, nice ma Saude lalle Hauwa kin haifu acikin Sahura tabbas ke jininta ce.
"Au da baki yarda ba kenan? zamu gamu ne wlh sai narama fin zagin da kikamin." Daga haka ta fice agidan batare da tajuya taga Saude ba.
Futar ta babu jimawa ta karasa gun Garba mai shago wanda yake kusa da gidansu
Garba mutum ne masifanfe, wanda shi ka' idarsa baya karbar bashi da rana sai dare mujinki yadawo tukum zeje da kansa yayi sallama ba kuma ze tafi ba sai anbashi kudinsa .
Yasha kashe auran mata da yawa dalilin haka sautari yaje to kuwa sai aure ya mutu atake.
Sallama ta masa tace "Garba mai shago barka da rana, ya kasuwa?"
yace "Hauwa kulu jidderh mai ladabin kare, daga ina haka ?"
Dariya jidderh tayi tace "Inna Saude ce tace kaban madarar ruwa guda biyu da kuma manyan bisket guda uku da leman kwalba guda biyu.
Garba yaji ciniki yace "amma de jidderh bak'i kukayi koh?"
Dariya Jidderh tayi tace "Eh, k'annan malama sukazo daga gashewa .
Yace "Allah sarki, nan Garba ya had'a duk abunda ta
Ba gida ta nufa ba, wani gu naga tabi a'lamun layin babu kowa cike tafiya tayi mara tsayi sosai sai kuma tazauna kan dakali ta bude kayan nna taci ta koshi tabar sauran, tasan yau yadda sukayi da Saude bazata bata abuncin ba dan haka tayi maganinta.
Tana zaune agun wata bakar mota tazo da tsaya gefanta
Bata ma kula ba, domin tayi nisa cikin tunanin abunda kuma zata shiryawa saude dan bata huce ba, taya zata dauki ruwan da zatayi wanka ta d'ibar mata, dan ta aiketa markade kafin ta dawo ta d'iba sabida renin wayo.
Wani gaye ne naga ya futo cikin motar amma fa ya hadu iyakar haduwa babu karya cikin haduwarsa cikin sauri
ya karasa gunta yayi ya mata Sallama
Juyawa tayi amma bata amsa ba.
Book Contact | INFORMATION |
---|---|
Book | HATSABIBIYA JIDDAH |
Author | Jidda bueaty |
Uploader | mrs littafan yaki |
Image Credit | Sufi Grapic |
Size | 130kb |
File | txt |
Date | 10 MAR 2023 |
Group | SUFI NOVEL |
Tages | Romantic Nove |
Post a Comment