DESCRIPTION
*NASARAWA GRA*
Fara ce doguwa, kyakkyawa ba mai muni ba mai dogon hanci. Bata da jiki, amma baza'a kirata siririya ba kuma ba mai ƙiba ba, ƴar daidai, sanye take cikin Swiss atampa baƙa mai touch ɗin blue da ratsin pink ɗinkin fitted gown, wanda ya bayyana ilahirin surar jikin ta.
Ɗaurin dake kanta Zahra Buhari ne, sai medium ɗin pink veil ƙirar Kashka data rufe bayan ta zuwa waist ɗin ta, yayin da gaban ke a buɗe. Chain bag ne maƙale a kafaɗar ta, inda ƙafar ta ke sanye da pink high heel mai tsayin dunduniya da igiya.
A natse take takowa harta iso farfajiyar gidan, gyatsine ta ɗanyi gami da tsaki kana tasa tafin hannun ta ta kare fuskar ta tana mai faɗin ''the weather's so hot''
Cigaba tayi da nufar makeken gate ɗin gidan ƙirar Tanzania harta iso gareshi, tun daga nesa mai gadin gidan (mal. Garba) keta kwarara mata kirari kamar ƴar sarki, murmushi kawai budurwar tayi, dan idan da sabo ta saba da hali irin nashi na ban dariya.
Allah ya ƙara nisan kwana matar manya, ganin ki alkhairi ne gaba salamun baya salamun, kariyar Ubangiji ta cigaba da yalwatuwa a duniyar ki shalelen Alhaji Babba!
Haka mal. Garba ya ringa kirari kamar Allah ya aiko shi,
2k ta zaro a jakar ta miƙa masa kana ta fice.
Karɓa yayi yana mai washe baki tare da dunƙule hannun hagun sa yana faɗin ''Allah ya ƙarama rayuwa albarka Hajiya Khansa'u, ya kuma ƙara nisan kwana''
Ko ta kanshi bata bi ba tayi gaba abinta, waige-waige ta somayi kafin ta hango wata Maroon ɗin mota ƙira Accord tana sheƙi fake aɗan nesa da gidan nasu, glass ɗin yaji dare (tinted).
Tsaki taja tana mai kauda kanta gefe.
Ganin bata da niyyar ƙarasowa yasa mai motar ƙarasawa gareta tare da sauke glass din motar.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!!! Allah yayi halitta anan, kyakkyawan matashi ne wanda ganin sa saida yasa alƙalami na faɗuwa, bazai gaza shekara 30 ba, duk da cewa ba fari bane amma tabbas yana da kyau, kwantacciyar baƙar suma ce kwance ta kanshi data haɗa da sajen gami da gyararriyar ƙasumbar dake fuskar sa, inda ya zuba mata manyan fararen oily eyes ɗin shi mai cike da kwarjini, inda fuskar sa ta ƙara yalwatuwa da siririn dogon hanci da madaidaicin baki.
Saida yaja iska ya fesar kafin ya fita, dan yasan halin kayar tashi sarai, tunda ta juya masa ƙeya fa bazata shiga ba.
Haba my love, fushin ya isa haka, ya kikeso nayi? Nayi iya bakin ƙoƙari na na fahimtar dake babu abinda ke tsakani na da Amreesh wlh, yarinyar yayan Mummy (mahaifiyar shi) ne kinji na rantse miki.
Hutu tazo gidan mu, shine tace jiya na ɗan fita da ita taga gari, wannan shine dalili.
Uhm! Naji, sai kuma me? Khansa'u ta faɗa cikin ƙunar zuciya kamar ta fashe da kuka.
Ajiyar zuciya matashin ya sauke yace ''Khansa'u''!
Cike da mamaki ta kalleshi, dan bai taɓa kiran sunan ta haka ba cikin kakkausar murya.
Baki yarda da Zayd ɗinki bane?
Juyawa tayi ta kuma cewa ''uhm''.
Murmushi yayi dan idan da sabo ya saba da shan wahala wajen rarrashin masoyiyar tashi, yanzun ma hakan ne ta kasance saida suka share kusan 40mins suna abu ɗaya, kafin ya samu ya shawo kanta. Ɗaukar ta yayi suka fita, basu tsaya ko ina ba sai munjibir park, dan ya santa da ƙaunar park, sosai taji daɗi kuwa yana ta yi mata hotuna tana dariya wanda ke ƙara bayyana kyawun fuskar tata.
Saida suka biya ta gidan sister ɗinshi dake zoo road kafin suka kamo hanyar gida, akan hanyar su ne aka soma wani faɗa tsakanin wasu samari dake unguwa daban-daban, sosai ake faɗa ana zubda jini ana kisa tamkar rai ba'a hannun kowa yake ba, ganin haka yasa Zayd ƙoƙarin yin reverse saidai kafin yakai gayi sun far musu.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai yake furtawa ita kuma tana kuka tana ƙoƙarin kiran Abban ta.... Ji kake tassssss ƙarar fashewar glass, glass ɗin dake gefen driver aka fasa inda yayi tsalle ya caki goshin Zayd ya shige ciki, ko shurawa baiyi ba, su kuma suka ci gaba da tarwatsa mota tare da tsiyaya mata fetur, saidai ashanar su taƙi kamawa hakan yasa sukayi gama abinsu... Faɗi kawai suke ''sai mun rama, baza'a dakemu da daki banza ba, sai mun ɗau fansa akan al'umma''.
Inda a ɓangaren Khansa'u kuwa girgiza Zayd kawai takeyi tana wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraron ta, sosai take kuka ta ɗauki kusan awa ɗaya tana abu ɗaya kafin ta fito daga motar zuwa lokacin abubuwan sun lafa, dan har al'ummar Annabi sun ɗan soma fitowa.
Kallon motar kawai tayi ta kuma rushewa da kuka ganin yadda ta tarwatse, wayar ta ta fiddo ta kira Abban ta har kira uku bai ɗagaba, nan ta maida akalar wayar kan lambar Mummy itama bata ɗaga ba, hakan yasa ta kira Aliyu ƙanin Zayd ta sanar masa halin da ake ciki tare da faɗa masa inda suke.
Hankali tashe ta tabbatar mata da gashi nan kuma kada subar wajen. Ba ɓata lokaci kuwa ya iso, kallo ɗaya zaka masa ka hango tsantsagwaron tashin hankali a fuskar sa, da ƙyar suka iya buɗe ƙofar mazaunin direban shida wasu matasa biyu.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Aliyu ya furta har sau uku, kafin wani zazzafan hawaye ya biyo kuncin sa, ya ƙurawa Zayd da fuskar sa ke ɗauke da murmushi ido, kamar ka kirasa ya amsa.
Lee (daman haka take kiran shi) mu kaishi asibiti mana.. ta faɗa cike da tashin hankali.
Girgiza kai kawai Aliyu yayi, dan kallo ɗaya yayiwa ɗan uwan nashi ya gano babu sauran numfashi a tare dashi....
Lee dan Allah ka ɗauko shi mu tafi, ta ƙara faɗa a karo na biyu cikin kuka mai ban tausayi.
Shi da ƴan samarin ne suka cicciɓeshi tare zuwa motar Aliyu, kowa na wajen fuskar shi cike da alhini, yayin da ƙwalla ta gangaro kan fuskar Aliyu, tunanin sa ɗaya idan har Zayd ya rasu tayaya zasu fara gayawa Daddy, daddy nada hawan jini faɗa mai irin wannan tashin hankalin akwai matsala, daidai sun ƙaraso hospital ɗin...
Nurses ne suka fito da gadon da za'a ɗaurashi a gurguje, cikin ƙanƙanin lokaci aka shiga dashi Emergency room....
______________________✍️
Babylor ce😘
By
Babylorh❤️
Marubuciyar;
Rushdah
Maraici Na
And now:
KHANSA'U
(The famous Arabic Poetess)
____Safa da marwa kawai Khansa'u keyi, tama rasa ina zata sa kanta, duk addu'ar da tazo mata yi kawai takeyi, zattauyi.
Aliyu ma da kallon tausayi kawai ya bisa kafin ya fito da wayar shi ya danna kiran Mummy, kamar kuwa jira take, bugu ɗaya ta amsa.
Aliyu wai ina Zayd ya shiga ne, ko kuma tare?
Amm Mummy Zayd ya samu accident ne, yanzu haka muna hospital an shiga dashi Emergency room.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, gani nan zuwa yanzu insha Allah.
Mum..., bai kai ga ƙarasawa ba ta katse wayar. Zama kawai yayi yana cigaba da addu'a Allah yaba Zayd lafiya.
Babu daɗewa mom ta ƙaraso tun kafin driver ya daidaita parking ma ta fito. Mata ce wadda aƙalla zatakai 47yrs, farace mai ɗan jiki mai matsakaicin tsayi, dan Aliyu ma ya fita, sanye take cikin Swiss Lace blue sai sky blue din flowers, kana ya yafa sky blue din mayafi babba.
Direct inda Emergency room yake ta nufa, nan taga halin dasu Aliyun ke ciki.
Dagudu Khansa'u tayi kanta tana rusar kuka marar ƙaran sauti, bubbuga bayan ta kawai Mummy takeyi alamar rarrashi har suka zauna. Sannu da zuwa yayi mata kafin ta soma tanbayar shi har yanzu likitan bai fito ba? Gyaɗa mata kai kawai yayi ba tare da ya iya cewa komai ba.
Suna hakane likitoci biyu suka fito daga ɗakin, ɗaya yana zare facemask ɗin fuskar sa ɗaya kuma yana sharce zufa, ɗaya daga cikin su Aliyu ya nufa yana mai tanbayar ya yaya jikin ɗan uwan nasa.
Girgiza kai kawai yayi tare da yi masa alama daya bishi office, gaba ɗaya suka tashi dan bin likitan amma ya takatar dasu, hakan yasa suka koma suka zauna Aliyu ya tafi.
Saida likitan yasha ruwa mai ɗan sanyi kafin ya fuskanci Aliyu..
Kayi haƙuri da abinda zan faɗa maka yanzu...tin kafin ya ƙarasa Aliyu yace ya mutu zakace koh?
Ɗan murmushin gefen baki yayi kafin yace ''a'a, yana da sauran rai, kuma munyi nasarar tsaida jinin dakeson haura masa ƙwaƙwalwa, and muna saka ran farkawar sa nan da awa huɗu, duk da bamu da tabbacin tashin sa, amma muna fatan ya tashi ɗin''.
Hawaye ne ya ziraro ma Aliyu na tausayin halin da Daddy zai shiga idan aka faɗa masa wannan labari.
Zagayowa likitan yayi tare da dafa kafaɗar sa yaɗan bubbuga kana yace ''so sorry pls, take heart kudai kawai kuci gaba da yi masa addu'a, Ubangiji Allah ya tashi kafaɗun sa ya bashi lfy mai ɗorewa''.
Ameen Aliyu ya amsa kana yayiwa doctor ɗin godia ya fita.
A hankali yake takawa ba tare da yasan inda yake sanya ƙafarshi ba, harya iso corridor ɗin dazai sada shi da Emergency section ɗin, tunda Khansa'u ta hango shi ta nufeshi da sassarfa harta isa gareshi tace ''Lee me likitan yace, ina ya Zayd ɗin, sunce mu shiga mu ganshi''? Ta jero masa tanbayoyin duk a lokaci ɗaya.
Hannun ta kawai ya kama zuwa inda Mummy ke zaune tare da sanar mata abinda likitan yace, amma bai faɗa mata basa da tabbacin tashin sa ba.
Har awanni huɗun nan suka cika babu wanda ya tashi a wajen sai Aliyu da yaje sallah, zuwa lokacin kuwa Hajia Mariya (mahaifiyar Khansa'u), da ƙannen ta biyu Haseena da Ayeesh, sai yayyin ta Zayyad (abokin Zayd ɗin) da Kuma Mahfouz (abokin Aliyu kenan) duk sun zo asibitin, harda ƙanwar su Zayd ɗin Ma'eesha.
A daidai lokacin ne wani likita ya fito tare da tanbayar mummyn patient ɗin, matsawa kusa Mummy tayi, likitan yace tabi bayan sa.
Ƙwance yake saman gadon marasa lafiya, ɗaure da wani abu a yatsan shi wadda batasan meye ba, sai hancin sa dake ɗauke da Oxygen, ga kuma kanshi dake ɗaure da bandage, hawaye ne kawai ya biyo fuskar Mummy (Allah sarki uwa😭).
Tana isa gareshi ya sauke Oxygen ɗin tare da furta kalmar 'Mummy' cikin murmushi. Murmushin itama ta masa dukda fuskar ta akwai hawaye ta rungume ɗan nata, kusan 2mins kafin ta sake shi, likitan yana ta kallon su cike da sha'awa da tausaya wa.
Ina sonki Mummy, shine abinda ya ƙara fitowa daga bakin shi har lokacin kuma Mummy yake kallo.
Nima Ina sonka son, Allah ya baka lfy.
Hmm kawai yace tare da kauda kansa gefe. Shigowar Khansa'u ne yasa Zayd juyowa ta kalleta, gaba ɗaya fuskar tayi fiyau ga kuma hawaye da yaƙi tsayawa.
Shine ni bakace a kirani ba ko ya Zayd, yanzu ma ture likitan nayi na shigo.
Gaba ɗayan su suka saka dariya harta isa inda suke, ya Zayd ya jikin naka?
Da sauki Baby, ya bata amsa cike da ƙauna.
A hankali a hankali kowa ya hallara a ɗakin duk suka zazzauna suna jimami, ƙarewa kowa na ɗakin kallo Zayd yayi kafin yace ''Mummy ina Daddy fah''?
Bai dawo ba Zayd, amma ya kirani zuwa anjima zai sauka insha Allah.
Saida suka kwashi kusan 2hrs a haka, akan ɗanyi nishaɗi da wasa da dariya har zuwa lokacin da Daddy ya iso.
Ba ƙaramin tashi hankalin Daddy yayi ba, ganin beloved son ɗinshi cikin wannan halin, amma saiya ɗau ƙaddara yayi masa addu'a kafin suka tafi masallaci shida sauran mazan.
Itama Mummy da Mummyn Khansa'u tashi sukayi suka nufi wajen Sallah, Haseena ma (mai bin Khansa'u) itama tashin tayi, ya rage daga Zayd, Khans, sai Ayeesh da Ma'eesha a ɗakin.
Khansa'u tana zaune gefen gadon riƙe da hannun Zayd tana matsa masa har zuwa wani ɗan lokaci.
Wata irin jijjiga yakeyi, gadon ma kaman zai ɓalle, ƙara damƙe hannun ta yayi ya mata wani irin riƙo mai azaba, Ayeesh da Ma'eesha ne suka fita kiran likita, ba daɗewa suka dawo da likitoci guda uku, da ƙyar da wuya suka raba hannun Zayd da Khansa'u, aka fita dashi daga ɗakin zuwa ICU (Intensive Care Unit).
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Sosai hankulan jama'a ya ƙara tashi, wa'inda suka dawo masallaci.
Sun ɗauki kusan awa ɗaya kafin suka fito gaba ɗayan su jiki a mace. Kafin akai ga yi musu magana sukayi saurin barin wajen tare da nufar office, da hanzari Daddy da ƴan sauran mazan sukabi bayan su har zuwa office.
Sosai likitan ke fargabar sanarwa Daddy dan yasan halin da yake ciki, shine likitan shi ma.
Amma Daddy sai ƙwarin gwiwa yake bashi na yin magana, hardai yayi jahadin faɗa musu cewa jijiyar ƙanshi ta tsinke kuma jini yayi nasarar taɓa ƙwaƙwalwar, wannan yana da nasaba da yawan magana da yayi da kuma rashin hutawa bayan farfaɗowar sa.. kuyi haƙuri Alhaji, every soul shall taste death, Allah Ubangiji yaji ƙansa da Rahma.
Tunda likitan ya soma magana Aliyu ya koma bayan Daddy ya tsaya, dan yasan wajibi ne wani abu ya faru, amma ga mamakin su ko gezau Daddy baiyi ba, saima hakuri da yake basu na rashin ɗan uwa da sukayi, sun yanke shawarar ƙin sanarwa matan har sai anje gida kada su cika asibitin.
Da ban baki da nasiha Daddy ya ɗauke su a motar shi zuwa gida, saida ya fara sauke su Mummyn Khansa'u da ƙannen ta amma furrrrr Khans tace saita ƙara haɗuwa da Zayd zata kwanta, babu yadda suka iya haka aka rabu da ita, suka tafi duka zuwa gidan su Zayd.
Ba daɗewa shima Aliyu suka dawo da gawar a motar sa, cikin ƙanƙanin lokaci labari ya karaɗe ko'ina, amma har zuwa lokacin babu wanda ya sani tsakanin Mummy da Khansa'u, gwara ma chan gidan su Khansa'u sunji labari wajen Zayyad.
Saida akayi masa sutura da komai amma an bari sai gobe a kaishi, kasancewar duhu daya fara wanzuwa.
Kiran da Mummy ta samu da gaisuwa da aka matane ya sanya ta a ruɗani, a sittin ta nufi ɗakin Daddy danjin ƙarin bayani..
Book Contact | INFORMATION |
---|---|
Book | khansa'u |
Author | Hafsat Ahmad beblor |
Uploader | mrs Littafan yaki |
Image Credit | Sufi Graphic |
Size | 246kb |
File | txt |
Date | |
Group | sufi publishe |
Tages | Romanti |
Post a Comment